Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aikawa takwaransa na kasar Ruwanda Paul Kagame sakon jaje, game da bala’in ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a kasar jiya Litinin 8 ga wata, inda ya bayyana damuwar sa game da aukuwar bala’in ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya shafi wasu sassa da dama na kasar Ruwanda a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata, ya kuma yi sanadin hasarar rayukan mutane da dukiyoyi masu yawa.
Shugaba Xi Jinping, ya ce a madadin gwamnatin kasar Sin da al’ummar Sinawa, yana juyayin rasuwar ‘yan kasar ta Ruwanda, yana kuma isar da alhinin sa ga iyalansu, da wadanda suka ji rauni, da kuma mutanen dake wuraren da bala’in ya adaba. Daga nan sai ya yi fatan Ruwanda za ta shawo kan wahalhalun da take fuskanta, tare da kuma sake gina muhallanta. (Mai fassarawa: Jamila)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp