A ranar 23 ga wata ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon ta’aziyya ga takwaransa na kasar Uganda Yoweri Kaguta Museveni kan harin da aka kai a wata makaranta a kasar Uganda wanda ya janyo hasarar rayuka.
Xi Jinping ya ce, ya kadu matuka da ya samu labarin cewa, ‘yan ta’adda sun kai hari a wata makaranta a yankin Kasese da ke yammacin kasar, lamarin da ya janyo hasarar rayuka da dama. A madadin gwamnati da jama’ar kasar Sin, ina mika ta’aziyyata ga wadanda abin ya shafa, da kuma jajantawa iyalan wadanda abin ya shafa da ma wadanda suka jikkata.
Shugaba Xi Jinping ya yi nuni da cewa, kasar Sin tana yin Allah wadai da duk wani nau’in ayyukan ta’addanci, kuma za ta ci gaba da nuna goyon baya ga kokarin Uganda na yaki da ta’addanci, da tabbatar da tsaro da zaman lafiya a kasar. (Ibrahim Yaya)