A kwanakin baya ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya amsa wata wasika da kungiyar musanyar dalibai da matasa ta Amurka da Sin da abokan hulda daga sassa daban daban na jihar Washington ta Amurka suka rubuta masa.
A wasikar tasa, shugaba Xi ya gode wa wadanda suka rubuta wasikar, bisa fatan alheri da suka nuna wa kasar Sin, na samun nasarar karbar bakuncin gasar wasannin daliban jami’o’in kasa da kasa ta lokacin zafi karo na 31 da ta gudana a birnin Chengdu a kudu maso yammacin kasar Sin da kuma gasar wasannin Asiya na Hangzhou a gabashin kasar.
Xi ya jaddada cewa, fata da tushen hadin gwiwar Sin da Amurka ta dogara ga jama’a, kana makomarta ta dogara ga matasa. Ya kara da cewa, yana fatan karin matasa daga kasashen Sin da Amurka, za su fahimci juna, da samun ci gaba tare, da zama jakadun tsara abokantaka, da ma ci gaba da ingiza raya dangantakar kasashen biyu. (Ibrahim Yaya)