A kwanakin baya shugaban kasar Sin Xi Jinping ya amsa wasikar da iyalan fursunonin sojojin Birtaniya da aka kama a jirgin ruwan dakon kaya na “Lisbon Maru” na kasar Japan suka aika masa, inda ya bayyana cewa, yana fatan karin abokan Sinawa na Birtaniya, za su ba da gudumowa ga huldar dake tsakanin Sin da Birtaniya.
Xi ya bayyana cewa, masuntan tsibirin Zhoushan dake lardin Zhejiang na kasar Sin sun ceto fursunonin sojojin Birtaniya da suka fada cikin teku daga jirgin ruwan “Lisbon Maru” sakamakon harbin sojojin Amurka, a shekarar 1942, lamarin da ya nuna cewa, kasar Sin da Birtaniya sun taba hada kai domin yaki da harin murdiya a yakin duniya na biyu, kana ya shaida cewa, akwai dadadden zumunci a tsakanin al’ummomin kasashen biyu.
Xi ya jaddada cewa, a bana ake cika shekaru 50 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Birtaniya, kuma a cikin wadannan shekaru 50 da suka gabata, an ciyar da huldar gaba yadda ya kamata, bisa kokarin da al’ummomin kasashen biyu suka yi.
A watan Oktoban shekarar 1942 ne, jirgin ruwan dakon kaya na “Lisbon Maru” wanda sojojin kasar Japan suke amfani da shi domin jigilar fursunoni sojojin Birtaniya sama da 1800 zuwa kasarsu, ya tashi daga yankin Hong Kong, amma sai sojojin Amurka suka harbi jirgin a kusa da tsibirin Zhoushan, inda fursunoni 843 suka rasa rayuka, sauran wasu 384 suka tsira, saboda daukin da masuntan tsibirin suka kai musu. (Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp