A cikin ‘yan kwanakin nan ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mayar da jawabi ga malamai da daliban tawagar musayar al’adu ta matasan Amurka masu buga wasan kwallon pickle daga gundumar Montgomery ta jihar Maryland, wadanda suka ziyarci kasar Sin a karkashin shirin gayyatar matasan Amurkawa 50,000 zuwa kasar Sin domin yin musaya da kuma nazarin karatu a cikin shekaru biyar.
Xi ya ce, makomar alakar Sin da Amurka ta dogara ce da matasa, yana mai bayyana fatan wakilan tawagar za su zama sabbin jakadu na sada zumunci a tsakanin kasashen biyu, da ba da gudummawa sosai wajen yaukaka zumuncin da ke tsakanin jama’ar kasashen biyu. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp