Shugaban kasar Sin, kuma babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping ya bayyana cikakken kwarin gwiwarsa game da farfadowar yankin arewa maso gabashin kasar Sin. Xi ya yi wannan tsokaci ne yayin rangadin sa a birnin Jinzhou na lardin Liaoning dake yankin.
Yayin ziyarar birnin a jiya Talata, shugaba Xi ya ce salon zamanantar da kasar Sin, na tattare da burin samar da walwala da jin dadi ga daukacin al’ummar kasar ba wai wasu tsiraru kadai ba.
Shugaban na Sin, ya kuma yi kira da a kara azama wajen aiwatar da dabarun farfado da yankin na arewa maso gabashin Sin, da ingiza tsarin raya masana’antu, ta yadda hakan zai dace da manufofin aiwatar da sauye sauye da samar da ci gaba a sabon zamani. Ya ce yana da cikakken kwarin gwiwa, game da farfadowar yankin arewa maso gabashin kasar Sin.
A yammancin jiya Talata Xi Jinping ya yi rangadin aiki a birnin Jinzhou, inda ya je dakin tunawa da yakin Liaoshen, domin waiwayen tarihin ‘yantar da yankin arewa maso gabashin kasar, daga baya ya ziyarci lambun shan iska na tafkin gabas.
Yayin ziyararsa, Xi ya saurari rahotannin da aka gabatar game da yaki da ambaliyar ruwa, da kare muhallin halittu masu rai da marasa rai, inda kuma ya ba da muhimmin umurni. (Mai fassarawa: Saminu Alhassan daga CMG Hausa)