A jiya Talata ne shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya bayyana cewa, babban hakkin da ya kamata a sauke game da batun Falasdinu shi ne a yi cikakkiyar aiwatar da kudurorin da kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya ya cimma matsaya a kai domin kawo karshen yakin da ake yi a yankin ba tare da bata lokaci ba.
A sakon taya murna da ya aike da shi ga bikin ranar nuna goyon baya ga al’ummar Falasdinawa na MDD da aka yi a ranar Talatar, shugaba Xi ya ce, kwakkwarar mafita game da wannan rikici ita ce a aiwatar da kudurin kafa kasashe biyu a yankin, da kuma daidaita matsalar Palastinu a siyasance. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp