Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada muhimmancin inganta biyayya ga jam’iyyar Kwaminis ta kasar a rundunar sojin kasar a sabon zamani, tare da samar da tabbaci ta fannin siyasa na gina rundunar soji mai karfi.
Xi Jinping wanda kuma shi ne sakatare janar na kwamitin kolin JKS kuma shugaban hukumar koli ta soja, ya bayyana haka ne yayin wani taro kan ayyukan da suka shafi siyasa a rundunar soji, wanda ya gudana a Yan’an na lardin Shaanxi dake arewa maso yammacin Sin, daga Litinin zuwa Laraba. (Fa’iza Mustapha)