Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya nemi hukumomi a dukkan matakai su bayar da fifiko ga tabbatar da kiyaye lafiya da dukiyoyin al’umma, kana su yi kokarin rage asara yayin da suke aikin tunkarar ambaliya da na tallafin saukaka radadin iftila’i.
Xi Jinping ya bayyana haka ne cikin wani muhimmin umarni da ya bayar yayin da ake ci gaba da fama da ruwan sama kamar da bakin kwarya a wasu yankunan kasar, ciki har da birnin Chongqing dake kudu maso yammaci, lamarin da ya haifar da dimbin asara.
Shugaban ya kuma bukaci hedkwatar hukumar tunkarar ambaliya da fari ta kasar da ma’aikatun kula da ayyukan daukin gaggawa da na albarkatun ruwa, su hada hannu da kara tuntuba da bincike, domin inganta gargadin wuri da ma hasashen yanayi.
Xi Jinping ya jaddada cewa, ya kamata jagororin jami’ai a dukkan matakai su jagoranci yaki da ambaliya, da sanya batun kiyaye lafiya da dukiyoyin al’umma a gaba da komai, kana su yi kokarin rage duk wata asara da za a iya samu. (Fa’iza Mustapha)