Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya karfafawa matasa masanan harkokin kasar Sin gwiwar zama manzonni domin inganta fahimtar juna tsakanin al’ummomin Sin da na sauran sassan duniya. Xi ya bayyana haka ne cikin amsar wasikar matasa masanan harkokin Sin 61 daga kasashe 51, wadanda za su halarci babban taron duniya kan harshen Sinanci da za a yi daga gobe Juma’a zuwa Lahadi, a birnin Beijing.
Xi Jinping ya bayyana farin cikin cewa ba Sinanci da al’adun Sin kadai wadanan matasa ke kauna ba, har da inganta fahimta game da harkokin Sin da koyi da juna tsakanin al’ummomi.
Ya kuma karfafa musu gwiwar ci gaba da gabatar da ainihin kasar Sin daga bangarori daban daban ga sassan duniya, tare da bayar da gudunmuwar hikima da karfin gina al’umma mai makoma ta bai daya ga dukkanin bil adama. (Mai fassara: FMM)














