Babban sakataren kwamitin kolin JKS kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping ya rubuta wani bayanin gabatarwa mai taken “Ci gaba a kan hanyar farfado da kasar Sin” a cikin wasu litattafai da za a wallafa masu taken “Farfado da kasar Sin”.
Cikin shafin gabatarwar, Xi ya yi nuni da cewa, koyi da darasin tarihi, al’adar gargajiya ce ta al’ummun Sinawa, kuma wallafa litattafan wata babbar al’ada ce da ya samu amincewar kwamitin kolin JKS, wanda yake da babbar ma’ana wajen ingiza farfadowar al’ummun Sinawa a halin da ake ciki yanzu. (Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp