Shugaban kasar Sin Xi Jinping a yau Talata ya gabatar da shawarwari guda hudu don hana rikicin kasar Ukraine kara tabarbarewa, da mai do da zaman lafiya tun da wuri.
Xi ya gana da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz dake ziyara a nan Beijing, kuma shugabannin biyu sun yi musayar ra’ayi mai zurfi kan rikicin Ukraine a tattaunawarsu.
- Sin Ta Raba Basira Da Karfinta Na Inganta Warware Rikicin Ukraine Ta Hanyar Siyasa
- Shekaru 2 Ke Nan Da Barkewar Rikici A Tsakanin Rasha Da Ukraine
Xi ya jaddada cewa, a halin da ake ciki a yanzu, domin hana rikicin kara tabarbarewa, ya kamata dukkan bangarorin su hada kai don dawo da zaman lafiya cikin sauri. Bisa wannan dalilin ne ya gabatar da shawarar ka’idoji guda hudu.
“Na farko ya kamata mu ba da fifiko wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da nisantar son rai. Na biyu kuma mu kwantar da al’amura, kada mu kara ruruwa wutar fitina. Na uku kuma mu samar da yanayin da za a maido da zaman lafiya, sannan mu guji kara tayar da hankula. Na hudu, ya kamata mu rage mummunan tasirin rikici kan tattalin arzikin duniya, tare da gujewa kawo tsaiko ga daidaton tsarin masana’antu da samar da kayayyaki a duniya.” (Mai Fassarawa: Yahaya Mohammed)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp