An gudanar da babban taron ayyukan tattalin arziki na tsakiya na shekara-shekara a birnin Beijing, daga ranar Laraba zuwa Alhamis, inda shugabannin kasar Sin suka yanke shawarar dora fifiko a kan ayyukan tattalin arziki a shekarar 2025.
Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gabatar da wani muhimmin jawabi a wurin taron.
- Kasar Sin Ta Gudanar Da Muhimmin Taron Tattalin Arziki Don Tsara Ayyukan 2025
- Bayan Sauke Mutane 7, Gwamna Yusuf Ya Kafa Kwamitin Neman Shawara
A cikin jawabin nasa, Xi ya yi bitar ayyukan tattalin arziki na shekarar 2024, kana ya yi nazari kan halin da ake ciki a fannin tattalin arzikin, da kuma tsara ayyukan da za a gudanar na tattalin arziki a shekara mai kamawa.
A yayin taron, an nunar da cewa, tattalin arzikin kasar Sin bai yi kasa a gwiwa ba ta ko wane fanni yayin da yake samun habaka a 2024, inda ya samu karfafawa mai zurfi ta fuskar samun ci gaba mai inganci, da kuma sa ran cimma nasarar aiwatar da manyan manufofi da ayyukan bunkasa tattalin arzikin da walwalar jama’a.
A yayin da yake la’akari da karuwar mummunan tasirin da wasu sauye-sauye na al’amuran waje suka haifar, da kuma matsaloli da kalubale da dama wadanda har yanzu ke fuskantar tafiyar da harkokin tattalin arzikin cikin gida, taron ya nuna cewa, yanayin goyon baya da muhimmin yanayin samun ci gaba na dogon zango da tattalin arzikin kasar Sin ke ciki suna nan daram ba su sauya ba.(Abdulrazaq Yahuza Jere)