Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jagoranci taron kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO) Plus a birnin Tianjin da ke arewacin kasar Sin a yau Litinin.
Xi ya gabatar da shawarar Tsarin Shugabanci na Duniya mai lakabin “GGI” a taron, inda ya bayyana wasu ka’idoji guda biyar domin tsarin na GGI wanda ya ce, na farko ya kamata mu bi tsarin daidaito a kan ‘yancin yankunan kasa sau da kafa, na biyu ya kamata mu kiyaye bin dokokin kasa da kasa, na uku ya kamata mu aiwatar da tsarin mu’amala da bangarori daban daban, na hudu kuwa ya kamata mu yi yekuwar amfani da tsarin da zai fi mayar da hankali a kan al’umma, kana na biyar ya kamata mu mai da hankali kan daukar matakai na hakika.
Xi kuma ya yi kira ga kasashe mambobin kungiyar SCO da su ba da gudummawa wajen kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya, da ci gaba da kiyaye ka’idojin zama ‘yan ba ruwanmu, da kauce wa tayar da husuma kuma ba tare da kulla makirci ga wani ba, da mikewa tsaye wajen sauke nauyin hadin gwiwa mai bude kofa ga kasashen duniya, da daukar matakai na kare daidaito da adalci a fagen kasa da kasa.
Kazalika, shugaba Xi ya yi kira da a yi kokarin hada karfi da karfe wajen kiyaye kyawawan sakamakon da aka samu bayan yakin duniya na biyu, da samar da karin alfanu ga daukacin bil’adama ta hanyar yin kwaskwarima ga tsarin shugabancin duniya, da gina al’umma mai makoma ta bai-daya ga bil’adama. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp