A yau ne, babban sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da shugaban jam’iyyar United Russia Dmitry Medvedev, wanda ya kawo ziyara kasar Sin bisa gayyatar da JKS ta yi masa.
Xi ya bayyana cewa, a cikin shekaru 10 da suka gabata, dangantakar dake tsakanin Sin da Rasha ta jure sauye-sauyen da duniya ta fuskanta, tare da kiyaye zaman lafiya da ci gaba mai inganci.
Shugaba Xi ya bayyana cewa, a shirye kasar Sin take ta hada kai da kasar Rasha, don ciyar da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu gaba a sabon zamani, da tabbatar da tafiyar da harkokin duniya cikin adalci da daidaito.
A nasa bangare, Medvedev ya mika sakon taya murnar sake zaben Xi a matsayin babban sakataren kwamitin kolin JKS, da kuma sakamakon da aka cimma a babban taron JKS karo na 20.
Bangarorin biyu sun kuma yi musayar ra’ayi, kan wasu batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya da ke shafarsu.(Mai fassara: Ibrahim Yaya)