A yau Alhamis 4 ga wannan wata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa da na kasar jamhuriyar Kongo Denis Sassou Nguesso wadanda suka zo kasar Sin domin halartar bikin murnar cika shekaru 80 da cimma nasarar yakin kin mamayar dakarun Japan, da yakin kin tafarkin murdiyya na duniya a babban dakin taron Beijing, fadar mulkin kasar.
Yayin ganawar, shugaba Xi da takwaransa na Zimbabwe sun sanar da cewa, za su daga alakar kasashensu zuwa ta samar da kyakkyawar makomar bil Adam ta bai daya a ko da yaushe, inda Xi ya nuna cewa, bana ake cika shekaru 45 da kafuwar huldar diplomasiya tsakanin Sin da Zimbabwe, don haka ya dace kasashen biyu su kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu, musamman ma a bangarorin gina manyan ababen more rayuwar jama’a, da hakar ma’adinai, da zuba jari, da gudanar da cinikayya.
A nasa bangare kuwa, shugaba Mnangagwa ya bayyana cewa, kasar Sin ta gabatar da shawarwari da dama, kuma tana taka rawar gani a harkokin kasa da kasa, don haka bangaren Zimbabwe ke fatan yin kokari tare da na Sin wajen kiyaye adalci a fadin duniya.
Yayin ganawa da takwaransa na jamhuriyar Kongo kuwa, Xi ya yi nuni da cewa, huldar dake tsakanin Sin da jamhuriyar Kongo ta zama misali na sada zumunta tsakanin Sin da Afirka. Kazalika, ana sa ran za a bude wani sabon shafi na hadin gwiwar cinikayya da zuba jari tsakanin kasashen biyu.
A nasa tsokaci kuwa shugaba Sassou, cewa ya yi kasar Sin ta shirya bikin murnar cika shekaru 80 da cimma nasarar yakin kin mamayar dakarun Japan, da yakin kin tafarkin murdiyya na duniya cikin nasara, lamarin da ya nuna aniyar hadin kai ta al’ummun kasar Sin ga duniya. Yana kuma fatan kara azama tare da kasar Sin wajen kare zaman lafiya a fadin duniya.
Har ila yau, a dai yau din shugaba Xi ya gana da babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar juyin juya halin jama’ar kasar Laos kuma shugaban kasar Thongloun Sisoulith, da shugaban kasar Vietnam Luong Cuong, da shugaban kasar Cuba Miguel Diaz-Canel, da firayin ministan jamhuriyar Slovakia Robert Fico, da shugaban kasar Serbia Aleksandar Vucic a nan birnin Beijing. (Mai fassara: Jamila)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp