Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugabar kwamitin wasannin Olympics na duniya (IOC) Kirsty Coventry da kuma shugaban kwamitin na karramawa Thomas Bach a Guangzhou, babban birnin lardin Guangdong da ke kudancin kasar Sin.
Xi ya nuna cewa, kasar Sin ta kasance mai himma, mai ba da kariya kuma mai yayata ruhin wasannin Olympics. Ya ce, gasar wasanni ta kasa ita ce babban bikin wasanni mafi girma a kasar Sin. Kuma yankunan Guangdong, Hong Kong da Macao ne suka hada hannu wajen shirya gasar wasannin ta kasa karo na 15. Ana kyautata zaton cewa, wannan gasar wasannin ta kasa ba wai kawai za ta bayyana sabbin nasarorin da kasar Sin ta samu a sabon zamani ba ne, har ma za ta nuna dimbin abubuwan ci gaba na zamanantarwa mai salo irin na kasar Sin a yankin Guangdong-Hong Kong-Macao.
A nasu bangaren, Kirsty Coventry da Thomas Bach sun bayyana cewa, kwamitin wasannin Olympics na duniya yana godiya ga kasar Sin saboda goyon bayan da take bayarwa na tsawon lokaci, kuma suna fatan ci gaba da karfafa hadin gwiwa da kasar Sin, tare da inganta ci gaban harkokin wasannin Olympics, da kara yada ruhin wasannin na Olympics a duk fadin duniya, da karfafa hadin kai tsakanin al’ummomin dukkan kasashe, da kuma inganta zaman lafiya a duniya.
Kazalika, duk dai a wannan rana, Xi ya gana da wakilan rukunonin gwajin al’amura da na daidaikun mutane a fannin wasanni na kasa da na gasar wasannin motsa jiki, kafin bude gasar wasannin ta kasa ta karo na 15 a Guangzhou. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














