Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwarorinsa na kasashen Kyrgyzstan Sadyr Zhaparov, da na kasar Turkmenistan Serdar Berdimuhamedov da na Tajikistan Emomali Rahmon a birnin Samarkand na kasar Uzbekistan.
Shugaba Xi Jinping ya bayyana a yayin ganawa da takwaransa na kasar Kyrgyzstan Sadyr Zhaparov a yau da safe cewa, kasar Sin ta kasance, a yanzu kuma a ko da yaushe za ta kasance aminiya kuma abokiyar huldar kasar Kyrgyzstan.
Yayin ganawarsa da takwaransa na kasar Turkmenistan Serdar Berdimuhamedov, shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, kasar Sin tana son ci gaba da sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar dake tsakaninta da Turkmenistan, domin moriyar jama’ar kasashen biyu.
A yayin da yake ganawa da takwaransa na kasar Tajikistan Emomali Rahmon kuwa, shugaba Xi ya bayyana cewa, akwai bukatar kasashen biyu wato Sin da Tajikistan, su ci gaba da goyon bayan juna, da samar da sakamakon da suka dace a dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. (Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)