A yau Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bukaci yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashin kansa da ya yi hobbasar gina Xinjiang na zamani mai ra’ayin gurguzu da ke kunshe da hadin kai, da kwanciyar hankali, da samun wadata, da arziki mai albarka, da raya al’adu da kyautata muhallin halittu, inda jama’a za su ci gaba da rayuwa da aiki cikin zaman lafiya da samun wadata.
Yayin da yake sauraren rahoton ayyukan kwamitin jam’iyyar JKS a yankin Xinjiang da gwamnatin yankin a yau 24 ga wata, shugaba Xi ya jaddada cewa, wajibi ne a kafa tubalin samar da albarkatu da masana’antu, da yin nazari sosai a game da turbar samar da ci gaba mai inganci da ta dace da sigogin yankin na Xinjiang.
Shugaban ya kara da cewa, ya kamata a bunkasa hade kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha da kirkire-kirkiren masana’antu, da habaka sabbin ginshikan ayyuka masu fa’ida daidai da yanayin cikin gida. Kazalika, wajibi ne a karfafa hade sha’anin al’adu da yawon bude ido tare da inganta ci gaban masana’antar yawon shakatawa na bangaren al’adu. Kuma ya kamata a karfafa ba da kariya da maido da muhallin halittu da karfafa cikakkun sauye-sauyen samar da ci gaba mara gurbata muhalli da habaka tattalin arziki da zamantakewa. (Abdulrazaq Yahuza Jere)