Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada bukatar inganta wani sabon tsarin da zai tattara albarkatu a fadin kasar, domin cimma dimbin nasarori a bangaren muhimman fasahohi na muhimman bangarori, tare da karfafa kokarin yin tsimin albarkatun.
Shugaba Xi ya bayyana haka ne a yau, yayin da yake jagorantar taro na 27 na hukumar koli mai kula da zurfafa gyare-gyare. (Fa’iza Mustapha)