Sakatare janar na kwamitin tsakiya na JKS, kuma shugaban kasar Xi Jinping, ya jaddada bukatar karfafa jagorancin rundunonin sojin kasar ta kowace fuska.
Shugaban ya bayyana haka ne jiya Litinin, yayin da yake jagorantar zaman nazari na ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na JKS, inda ya yi kira da a inganta raya ayyukan rundunonin soji ta hanyar inganta shugabancinsu.
Zaman ya wakana ne gabanin Ranar Rundunar Sojin ’Yantar Da Al’ummar Sinawa dake ya fado a ranar 1 ga watan Augusta, kowace shekara. (Mai Fassarawa: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp