Babban sakataren kolin kwamitin tsakiya na JKS Xi Jinping, ya jaddada muhimmancin karfafa tsarin shari’a mai nasaba da kasashen ketare. Shugaba Xi ya yi kiran ne yayin da yake jagorantar zaman nazari na hukumar siyasa na babban kwamitin JKS a jiya Litinin.
Cikin jawabin da ya gabatar, Xi ya fayyace bukatar kirkiro tsare-tsaren jagoranci bisa doka, da samar da kyakkyawan yanayi ga sassan waje, na bunkasa zamanantarwa irin ta kasar Sin. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp