Shugaban kasar Sin kuma sakatare janar na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin(JKS) Xi Jinping, ya bukaci a yi kokarin inganta samar da ingantattu kuma wadatattun guraben ayyukan yi, tare da ci gaba da tabbatar da samun gamsuwa da farin ciki da tsaro tsakanin ma’aikata.
Xi ya yi kiran ne a jiya Litinin, lokacin da yake jagorantar zaman nazari na ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS.
- ‘Yansanda Sun Kama Ƙasurgumin Ɗan Bindiga, Sun Kwato Kudin Fansa A Kaduna
- Gwamna Uba Sani Ya Kaddamar Da Rabon Kayayyakin Amfanin Gona Ga Manoman Kaduna 40,000
A cewarsa, dole ne kasar Sin ta aiwatar da ra’ayin samar da ci gaba dake mayar da hankali kan al’umma da kyautata inganci da wadatar ayyukan yi ta hanyar dabaru na musammam da za su kai ga samar da ayyukan yi.
Yayin zaman, shugaba cibiyar nazarin harkokin kwadago da kula da al’umma ta kasar Sin Mo Rong, ya gabatar da jawabi kan batun na samar da ingantattu kuma wadatattun ayyukan yi, tare da gabatar da shawarwari. Kuma bayan sauraron jawabin, mahalarta sun tattauna kan shawarwarin.
Tun bayan babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18 a shekarar 2012, shugabancin jam’iyyar ya ba batun samar da aikin yi muhimmanci a harkokin jagorantar kasar, inda a kowacce shekara ake samar da guraben ayyukan yi miliyan 13 a matsakaicin mataki. (Fa’iza Mustapha)