Babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira da a ci gaba da yin gyare-gyare a jam’iyyar, da samun nasara a yakin da ake yi da matsalar cin hanci da rashawa.
Xi, wanda kuma shi ne shugaban kasar Sin, kuma shugaban rundunar sojojin kasar, ya bayyana aàhaka ne, yayin da yake jawabi ga cikakken zaman taro karo na uku na kwamitin kolin ladabtarwa na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 20. (Mai fassara: Ibrahim)