A yau Litinin ne shugaban kasar Sin, kuma babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya jaddada bukatar yin aiki tukuru wajen aiwatar da cikakkun manufofi, na ingiza managarcin jagorancin jam’iyyar bisa kyawawan akidu.
Shugaba Xi ya yi kiran ne cikin tsokacin da ya yi, lokacin da yake jagorantar taron nazari na jami’an hukumar siyasar na kwamitin kolin JKS. (Saminu Alhassan)