Kwanan nan, mamban hukumar siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin wato JKS, kuma sakatarorin sakatariyar hukumar, da mamban kungiyar JKS na zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin NPC, majalisar gudanarwa kuma majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin CPPCC, da kuma darektan kwamitin JKS na kotun jama’a ta koli kuma hukumar gabatar da kararraki ta koli, sun ba da rahotannin tantance nasarorin aiki ga kwamitin kolin JKS da kuma babban sakatarensa Xi Jinping.
Xi ya duba rahotannin kuma ya gabatar da muhimman bukatu. Yana mai jaddada cewa, shekarar bana ita ce shekarar karshe ta shirin shekaru biyar-biyar na 14, kuma muhimmiyar shekara ce ta kara zurfafa yin gyare gyare. Dole ne a mai da hankali cikin natsuwa game da kalubalen da sauye-sauyen yanayi na cikin gida da na waje suka haifar, da tabbatar da ingantaccen ci gaba, da habaka bude kofa ga waje a babban mataki, da inganta rayuwar jama’a a kai a kai. Dole ne mu dauki sabbin nauyi kuma mu yi sabbin ayyuka a sabuwar tafiya ta inganta zamanantarwa irin ta kasar Sin. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp