Yau ne, babban sakataren Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping, da sauran mambobin zaunannen kwamitin ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na JKS karo na 20 da suka hada da Li Qiang da Zhao Leji, da Wang Huning, da Cai Qi, da Ding Xuexiang da Li Xi, suka bayyana a gaban ‘yan jaridu a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.
Babban sakataren kwamitin kolin Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping, ya bayyana cewa, babban taron wakilan JKS na karo na 20, shi ne babban taro na kara daga turar jam’iyyar, da hada karfi da karfe, da inganta hadin kai da kuma sadaukarwa.
Xi ya bayyana cewa, ya kamata jam’iyyar ta yi wa jama’a aiki ta kuma dogara ga jama’a a kan tafiyar da aka sanya a gaba.
Xi ya ce, ya kamata jam’iyyar ta ci gaba da yi wa kanta gyare-gyare kan wannan tafiya da aka sanya a gaba. Yana mai cewa, kasar Sin za ta kara bude kofarta ga kasashen ketare, da sa kaimi ga zurfafa yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje a dukkan fannoni.
Ya kara da cewa, za mu yi aiki da sauran al’ummomin kasashe, don daukaka dabi’un bil-Adama na zaman lafiya, da bunkasuwa, da nuna adalci, da demikiradiya da ‘yanci, da kiyaye zaman lafiya a duniya, da bunkasa ci gaban duniya, da ci gaba da gina al’umma mai makomar bai daya ga daukacin bil-Adama. (Ibrahim)