Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada bukatar zage damtse wajen ganin an gina kyakkyawar kasar Sin daga dukkan fannoni, da kuma hanzarta ci gaban zamanantarwa, mai kunshe da zaman jituwa tsakanin bil-Adama da muhalli.
Xi, wanda shi ne babban sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban kwamitin kolin soja, ya bayyana haka ne a yayin taro kan kare muhalli da aka gudanar daga jiya Litinin zuwa Talatar nan. (Mai fassara: Ibrahim)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp