Babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya jaddada kara kaimi wajen shiga cikin garambawul na hukumar cinikayya ta duniya wato WTO, da kuma kyautata ikon gudanar da ayyukan bude kofa ga waje.
Xi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jagorantar taron nazari na ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS a yau Laraba.
Ya ce, muna bukatar fahimtar muhimmanci da gaggawar shiga cikin garambawul na kungiyar cinikayya ta duniya. Tare da karin nauyi na tarihi da kuzarin kirkire-kirkire, ya kamata mu shiga cikin sake fasalin Hukumar Cinikayya ta Duniya da daidaita ka’idojin tattalin arziki da dokokin cinikayyar kasa da kasa, da inganta yin kwaskwarima mai zurfi da ci gaba mai inganci ta hanyar kyautata bude kofa ga kasashen duniya (Yahaya).