Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada muhimmancin inganta tsarin gudanar da harkokin kamfanoni a zamanance mai halayyar musamman ta Sin, tare da yayata samar da muhalli budadde, na yin kyakkyawar takara a fannonin kirkire kirkiren kimiyya da fasaha.
Shugaba Xi ya yi wannan tsokaci ne a Talatar nan, yayin da yake jagorantar taro karo na 5, na hukumar koli ta zurfafa sauye sauye daga dukkanin fannoni, karkashin kwamitin kolin JKS na 20, wanda yake shugabanta. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp