Kwanan baya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyarar aiki a jihar Ningxia ta kabilar Hui mai cin gashin kanta dake arewa maso yammacin kasar. A yayin ziyararsa a jihar, ya jaddada cewa, ya kamata a aiwatar da sabbin ra’ayoyin neman bunkasuwa yadda ya kamata a jihar Ningxia, domin kare muhalli a wuraren da ke kewayen Rawayen Kogi da kafa yankin neman ci gaba mai inganci, ta yadda za a inganta bunkasuwar yankin baki daya, da kuma zurfafa aikin yin kwaskwarima da habaka bude kofa ga waje, da raya birane da samun farfadowar yankunan karkara, da kuma karfafa hadin gwiwar mutane na kalibu daban daban da samun wadata tare. Haka kuma, ya kamata a gaggauta aikin gina jihar Ningxia mai kyau, wadda ta samu bunkasuwar tattalin arziki, da hadin gwiwar al’umma, da kyakkyawan muhalli, da kuma wadatar al’umma. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp