Shugaban kasar Sin, kuma babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya jaddada muhimmancin samar da ci gaban jagoranci mai inganci da karko a yankuna kan iyakokin kasa.
Shugaba Xi, ya bayyana hakan ne a jiya Litinin, yayin da yake shugabantar taron ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, yana mai cewa zamanantar da tsarin aiki, da karfafa sanin makama a fannin jagoranci a wadannan yankuna, bangare ne mai matukar muhimmanci karkashin aniyar kasar Sin ta zamanantar da kai. (Mai fassara: Saminu Alhassan)