Babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira da a yi tsayin daka wajen yin nasara na dogon lokaci kan yaki mai tsauri da cin hanci da rashawa.
Xi, wanda kuma shi ne shugaban kasar Sin, kuma shugaban kwamitin kolin soja na kasar, ya jaddada tsauraran tsarin gudanar da jam’iyyar tare da ruhin yin gyare-gyare a lokacin da yake jawabi ga cikakken zama na hudu na kwamitin kolin JKS mai kula da ladabtarwa karo na 20. (Mai fassara : Mohammed Yahaya)