Shugaban kasar Sin Xi Jinping a yau Alhamis ya yi kira ga dakarun kasar da su karfafa alkiblar aikinsu, da zurfafa gyare-gyare da habaka kirkire-kirkire, don inganta kwarewarsu a sabbin fannoni.
Xi, ya bayyana hakan ne yayin da yake halartar taron tawagar sojojin ‘yantar da jama’a da kuma rundanar ‘yan sandan kasar a zama ta biyu ta majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14, wato majalisar dokokin kasar. (Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp