Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai rangadin aiki a birnin Shanghai na gabashin kasar Sin daga ranar Talata zuwa Laraba.
Ya ziyarci cibiyar hada-hadar kudi ta Shanghai, da bikin baje kolin ci gaban kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha na Shanghai, da gidan masu gina sabon zamani da manajoji a yankin Minhang don fahimtar kokarin Shanghai na inganta gasa a matsayinta ta cibiyar hada-hadar kudi ta kasa da kasa, da inganta aikin cibiyar kimiyya da fasaha ta kasa da kasa, da gina gidajen haya masu araha. (Mai fassara: Yahaya)