Larabar nan ce, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ziyarci birnin Meishan na lardin Sichuan dake yankin kudu maso yammacin kasar.
Da safiyar yau, Xi ya ziyarci kauyen Yongfeng da San Su Ci, wurin tunawa kuma tsohon mazaunin Su Xun da ‘ya’yansa maza guda biyu Su Shi da Su Zhe, mashahuran mutane uku wajen adabi na zamanin daular Song ta Arewa (960-1127).
Xi ya kuma fahimci kokarin da ake yi wajen bunkasa manyan filayen noma, da bunkasa noman hatsi, da inganta farfado da yankunan karkara, da kiyaye muhimman matakan kandagarki da dakile yaduwar COVID-19, da kiyaye kayayyakin tarihi da na al’adu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp