Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira da a inganta yanayin tafiyar da tattalin arzikin duniya da gina shi ta hanyar hadin gwiwa.
Xi Jinping ya bayyana haka ne cikin muhimmin jawabin da ya gabatar mai taken “Hada Hannu Domin Tafiyar da Tsarin Tattalin Arzikin Duniya Bisa Adalci da Daidaito,” yayin zama na II na taron kungiyar G20 karo na 19, a jiya Litinin.
- Kamata Ya Yi Sin Da Amurka Su Mai Da Hankalinsu A Kan Ci Gaban Duniya
- An Kashe Mutum 50, An Sace 170 Cikin Wata 7 A Kaduna
A cewarsa, a matsayinsu na manyan masu bayar da rance, ya kamata cibiyoyin kudi na kasa da kasa da kamfanoni da daidaikun ‘yan kasuwa masu bayar da bashi, su shiga cikin shirin rage yawan basussuka da tsawaita lokacin biya, ga kasashe masu tasowa.
Ya kuma yi kira da a inganta tsarin tafiyar da harkokin kudi na duniya da gina tattalin arzikin duniya mai karko. Yana cewa, akwai bukatar hada hannu domin tabbatar da daidaiton tsarin kasuwar hada hadar kudi na duniya da kare yaduwar sauye-sauye manufofin kudi na cikin gida zuwa sauran yankuna. Haka kuma, ya kamata kasashe masu wadata su sauke nauyin dake wuyansu a wannan bangare.
Har ila yau, shugaba Xi Jinping ya yi kira da a gina tattalin arzikin duniya mai bude kofa, yana cewa, “ya kamata mu ingiza yi wa hukumar kula da cinikayya ta duniya (WTO) garambawul, da adawa da kariyar cinikayya da ra’ayin bangare daya, da dawo da tsarin warware takkadama mai inganci nan bada jimawa ba, da sanya yarjejeniyar saukaka zuba jari domin samun ci gaba, cikin tsarin dokokin WTO da kuma cimma matsaya daya kan yarjejeniyar cinikayayya ta intanet.
Ya kuma yi kira da a inganta tsarin tafiyar da harkokin dijital da gina tattalin arziki dake mayar da hankali ga kirkire-kirkire. Ya ce akwai bukatar inganta tsarin jagoranci da hadin gwiwa a bangaren kirkirarriyar basira wato AI, domin tabbatar da kowa ya amfana da fasahar ta AI, ba kawai kasashe da mutane masu wadata ba.
Bugu da kari, ya yi kira da a kyautata yanayin kula da muhallin duniya da gina tsarin tattalin arziki mai dacewa da kare muhalli. Ya ce “sauyawa zuwa amfani da makamashi mai tsafta da wadatar makamashin, babban batun ne. Don haka ya kamata mu yi amfani da dabarar nan ta karfafa sabon, kafin kawar da tsoho,’ tare da maye gurbin tsohon makamashin da sabo, ta hanya mai tsari da dorewa.” (Fa’iza Mustapha)