Da yammacin yau Litinin ne ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya gudanar da taron nazari karo na 22, kan yadda za a sa kaimi ga mayar da addinan Sin zuwa addinan dake da salo na kasar.
Yayin da ya jagoranci taron, babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya jaddada cewa, “Ya kamata mu tattara, da kuma amfani da darussan tarihi, mu mayar da hankali kan hakikanin ayyukan addinai na kasa, da sa kaimi ga mayar da addinan Sin zuwa addinan dake da salo na kasar, da kuma jagorantar addinai don daidaita al’umma mai ra’ayin gurguzu”.
Xi Jinping ya kara da cewa, ana bukatar sa kaimi ga dunkulewar addinan kasar Sin, tare da kyawawan al’adun gargajiya na kasar bisa wayewar kan al’ummar kasar na tsawon shekaru dubu 5, da kuma karfafa fahimtar ma’aikatan dake gudanar da harkokin addinai, da masu bin addinai, kan amincewa da al’adun kasar Sin.(Safiyah Ma)