A yau Alhamis, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya mika jaje ga shugabannin kasashen Azerbaijan Ilham Aliyev da na kasar Rasha Vladimir Putin da kuma na Kazakhstan Kassym-Jomart Tokayev bisa asarar rayukan mutane da aka yi a hadarin jirgin saman kamfanin Azerbaijan. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)