A yau Alhamis ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon taya murna ga dandalin tattaunawa na kasa da kasa na Imperial Springs na shekarar 2024. Xi ya yi nuni da cewa, tun bayan kafuwar dandalin shekaru 10 da suka gabata, dandalin ya nace kan ba da shawarar yin hadin gwiwa tsakanin bangarori daban-daban, da gudanar da tattaunawa mai zurfi kan batutuwan da suka shafi harkokin mulkin duniya, da yawaita yayata shawarwari na kasar Sin, da kuma taka rawa mai kyau wajen inganta mu’amala da fahimtar juna tsakanin Sin da kasashen duniya.
Xi ya jaddada cewa, a cikin wannan duniya mai cike da sauye-sauye da rikice-rikice masu nasaba da juna, zaman lafiya da ci gaba su ne burin bai daya na dukkan jama’a.
- An Cika Shekaru 10 Da Kaddamar Da Kashin Farko Na Janyo Ruwan Layin Gabas Da Tsakiya Daga Kudancin Sin Zuwa Arewacinta
- Sin Na Shirin Kafa Sassan Likitancin Gargajiya Kimanin Dubu 10 Zuwa Shekarar 2029
Xi ya ci gaba da cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da sauran kasashen duniya bisa ruhin “sa kaimi ga hadin kan duniya”, da tabbatar da daidaici da adalci wajen kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya, da yin riko da hadin gwiwar samun nasara tare don sa kaimi ga ci gaban duniya mai dorewa, da kuma himmatuwa wajen hada kai da fahimtar juna don ciyar da wayewar kan dan Adam zuwa wani sabon matsayi.
A yau Alhamis ne aka bude taron na “dandalin tattaunawa na kasa da kasa na Imperial Springs na shekarar 2024” a birnin Madrid na kasar Sifaniya. (Mohammed Yahaya).