Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika sakon taya murna ga zaman taro na 15 na kwamitin sada zumunta da bunkasa zaman lafiya da ci gaba tsakanin Sin da Rasha, da aka gudanar yau Asabar a birnin Vladivostok na Rasha.
Xi ya jaddada cewa, tun kafuwarsa a cikin shekaru 28 da suka gabata, kwamitin sada zumunta da bunkasa zaman lafiya da ci gaba tsakanin Sin da Rasha, ya nace ga bin turbar ainihin burin da ake so da manufar karfafa sada zumunta da hadin gwiwa, tare da cikakkyar hidimta wa dukkan yanayin dangantakar da ke tsakanin Sin da Rasha, da kafa ginshiki mai karfi na raya huldar kasashen biyu a tafarkin ra’ayin al’umma. Ana fatan kwamitin zai dauki wannan taro a matsayin wata dama ta taka rawar gani a matsayin babbar kafa ko hanyar gudanar da mu’amalar jama’a a tsakanin kasashen biyu, da kuma rubuta wani babi na sada zumunta a kan fahimtar juna da hadin kai a tsakanin al’ummomin kasashen biyu a sabon zamani.
Kazalika, duk dai a wannan rana, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya gabatar da jawabin taya murna ga zaman taron. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp