A yau Talata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tashi daga birnin Beijing don halartar taron kolin BRICS karo na 16 a birnin Kazan na kasar Rasha, bisa gayyatar da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya yi masa.
Tawagar Xi ta kunshi Cai Qi, mamban zaunannen kwamitin kula da harkokin siyasa na kwamitin kolin jamiyyar kwaminis ta kasar Sin, kana darektan babban ofishin kwamitin Kolin JKS, da Wang Yi, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, kana ministan harkokin wajen kasar Sin. (Mai Fassara: Mohammed Baba Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp