A yau Litinin ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayyana cewa, tarihi da gaskiyar da take baro-baro a fili sun nuna cewa, Sin da Rasha makwabta ne nagari da ba za a iya wancakalar da su a gefe ba, kuma aminai na hakika da ke tare da juna walau cikin dadi ko jarabta, kana sun kasance masu goyon bayan juna da samun ci gaba tare.
Xi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ta wayar tarho.
- Thomas Bach: Kasar Sin Ta Ba Da Gagarumar Gudummawa Ga Bunkasa Wasannin Olympics
- Gwamnatin Katsina Ta Kashe Naira Biliyan 5.7 Wajen Sayen Awaki 40,000 Domin Raba Wa Mata
Ya kuma kara da cewa, dangantakar da ke tsakanin Sin da Rasha tana samun karfafawa daga cikin gida da kuma wata daraja ta musamman, kana ya ce, ba su kulla zumuncinsu saboda wani ba, don haka babu wani daga gefe da zai iya batawa ko katsalandan.
Xi ya shaida wa Putin cewa, duk da sauye-sauyen da ake samu a yanayin duniya a yanzu, dangantakar Sin da Rasha za ta ci gaba da kasancewa cikin sauki, wadda za ta taimaka wa juna wajen samun ci gaba tare da farfado da juna, da tabbatar da kwanciyar hankali da kara karfafa huldar kasashen duniya ta kyakkyawar hanya.
Xi ya kuma bayyana cewa, kasar Sin tana farin cikin ganin kasar Rasha da bangarorin da abin ya shafa sun yi kokarin kawo karshen rikicin Ukraine, yana mai jaddada cewa, tun a farkon rincabewar rikicin na Ukraine, ya gabatar da shawarar “abubuwa hudu da suka kamata a yi” da sauran muhimman shawarwari na lalubo bakin zaren warware rikicin.
Shugaba Xi ya kuma yi nuni da cewa, a watan Satumban bara, Sin da Brazil, tare da wasu kasashe masu tasowa, sun kafa kungiyar abokan zaman lafiya game da rikicin kasar Ukraine, don samar da sarari da kuma ingantattun sharudda domin karfafa warware rikicin a siyasance. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp