Yau Asabar ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon taya murna ga Bola Tinubu kan zabensa a matsayin shugaban Najeriya.
Xi ya yi nuni da cewa, Najeriya muhimmiyar abokiyar hulda ce ta kasar Sin a nahiyar Afirka. A ‘yan shekarun baya-bayan nan, alakar dake tsakanin kasashen biyu ta samu kyakkayawan ci gaba tare da samun sakamako mai kyau wajen yin hadin gwiwa a aikace a fannoni daban daban, kuma kasashen biyu sun nuna goyon baya ga juna kan batutuwan da suka shafi muhimman moriyarsu, da hadin gwiwa a harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya.
Shugaba Xi ya ce, yana mai da hankali matuka kan raya dangantakar dake tsakanin Sin da Najeriya, kuma yana son yin aiki tare da shugaban kasar da aka zaba, Bola Tinubu, don ciyar da dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Najeriya zuwa wani sabon matsayi. (Ibrahim)