Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya umarci gudanar da dukkan kokari na bincike da kuma ceto domin takaita mutuwar mutane, bayan aukuwar wata ruftawar kasar da ta nutsar da gidaje 10, da bacewar fiye da mutane 30 a lardin Sichuan da ke kudu maso yammacin kasar Sin, a yau Asabar.
Shugaba Xi ya bayar da umarnin ne bayan ruftawar kasar da misalin karfe 11:50 na safiyar yau Asabar, a kauyen Jinping da ke gundumar Junlian a birnin Yibin. (Abdulrazaq Yahuza Jere).