Albarkacin ranar bikin girbi ta manoman kasar Sin karo na 6, shugaban kasar Xi Jinping, ya gabatar da sakon taya murnar wannan biki ga daukacin manoman kasar, da ma tarin jami’ai dake aiki a fannin noma da raya karkara a dukkanin fadin kasar.
Cikin sakon na sa, Xi ya ce a bana, al’ummar Sinawa ta shawo kan bala’o’i irin su ambaliyar ruwa, da fari a wasu yankunan, a hannu guda kuma, ana fatan samun yabanya mai yalwa, wanda hakan zai karfafa tallafin da ake nema na ingiza farfadowar tattalin arzikin kasar mai dorewa.
Kaza lika shugaba Xi ya jaddada cewa, kamata ya yi dukkanin sassan ma’aikatun gwamnati, su goyi baya ga farfadowar yankunan karkara, da gaggauta aiwatar da matakan bunkasa harkokin noma, da zamanantar da yankunan karkara, kana su yi duk mai yiwuwa, wajen fadada damammakin manoma na samun karin kudaden shiga, ta yadda za su kara samun wadata, da karin kyautatuwar rayuwa. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp