Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira da a gudanar da aikin tantance harkar kudade bisa tsarin sa ido mai inganci, domin samar da kariya ga ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasar mai inganci.
Xi ya bayyana hakan ne a wani umarni na baya-bayan nan game da aikin tantance harkar kudade, inda ya mayar da aikin tantance harkar kudade a matsayin wani muhimmin bangare na tsarin sa ido na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin da kuma kasar ta Sin.
- Gobara Ta Yi Ɓarna A Kwara, Shaguna 7 Sun Ƙone
- Binciken Jami’ar Bayero Ya Gano A Hoton Yatsa Za A Iya Gane Mai Cutar Daji – Farfesa Darma
Xi ya kara da cewa, a cikin ‘yan shekarun nan, hukumomin bincike kan hada-hadar kudi sun taka rawar gani sosai wajen kara inganta ci gaban tattalin arziki, da kiyaye tsaron tattalin arzikin kasar, da bayyana hadurra da tattalin arzikin ka iya fuskanta, da kuma ciyar da yaki da cin hanci da karbar rashawa gaba.
Da yake karin haske game da shugabancin kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin kan aikin tantance harkar kudade, shugaba Xi ya jaddada cewa, kamata ya yi hukumomin binciken su mai da hankali kan ayyukansu na asali da muhimman ayyukansu, da zurfafa yin gyare-gyare, da yin kirkire-kirkire, da kuma karfafa ci gaban kansu. Ya kuma yi kira da a samar da cikakken tsarin sa ido kan aikin aikin tantance harkar kudade daga matakin koli kuma na bai daya, mai karfin iko da inganci. (Mohammed Yahaya)