A yau Laraba ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira da a kara azamar ingiza ci gaban yankin tsakiyar kasar Sin daga babban mafari.
Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban hukumar aikin soja ta kasar, ya yi kiran ne cikin jawabin da ya gabatar yayin taron karawa juna sani game da yadda za a zaburar da ci gaban yankin tsakiyar kasar Sin a sabon zamani.
Bugu da kari, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada cewa, manufar gudanar da makaranta, ba wai don daukaka darajar dalibai kawai ba, har ma da yi musu jagora wajen yi wa kasa hidima.
Xi ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ziyarci daya daga cikin harabar jami’ar farko ta Hunan a ranar Litinin din da ta gabata yayin wani rangadi da ya kai birnin Changsha, babban birnin lardin Hunan na tsakiyar kasar Sin.
Kazalika, yayin rangadinsa a wani kauye a birnin Changde da ke lardin Hunan na tsakiyar kasar Sin a ranar Talata, Xi ya saurari rahoto daga jami’an kauyen kan kokarin da yankunan ke yi na saukaka wa masu aiki a matakin farko dawainiyar aiki a yankunan karkara a ’yan shekarun nan. (Saminu Alhassan, Mohammed Yahaya)