Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga daukacin jama’ar kasar Sin da su yi aiki tukuru, tare da ingiza wanzar da zamanantarwa irin ta Sin. Xi, wanda kuma shi ne sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban hukumar zartarwar rundunar sojojin Sin, ya yi kiran ne yayin taron bikin cika shekaru 76 da kafuwar janhuriyar jama’ar kasar Sin, wanda ya gudana yau Talata a babban dakin taruwar jama’a dake birnin Beijing.
Shugaba Xi, ya jaddada cewa a gabar da yanayin harkokin duniya ke saurin sauyawa cikin sama da karni guda, dole ne a yi aiki tukuru wajen yayata akidun bai daya na dukkanin bil’adama, da aiwatar da tsarin cudanyar mabanbantan sassa, da ingiza aiwatar da shawarwarin bunkasa ci gaban duniya, da shawarwarin tsarin shugabancin duniya, da shawarwarin wayewar kan duniya, da shawarwarin shugabancin kasa da kasa, da aiki tare da dukkanin kasashe wajen gina al’ummar duniya mai makomar bai daya ga dukkanin bil’adama.
Kasar Sin tana gudanar da bikin ranar kafuwarta a ranar daya ga watan Oktoba. (Mai fassara: Saminu Alhassan)