Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon taya murnar kafa kungiyar kasa da kasa ta tattauna batutuwan da suka shafi kafar intanet.
Xi Jinping ya jaddada cewa, kafar intanet na da alaka da makomar bil adama. Kuma Sin ta shirya hada hannu da kasa da kasa wajen daukar kungiyar a matsayin wata muhimmiyar dama ta inganta tabbatar da kafar ta intanet ta kasance buddadiya mai cike da tsaro da tabbatar da adalci, kuma mai kwari da kuzari, ta yadda jama’a a fadin duniya za su amfana.
An gudanar da taron kaddamar da kungiyar ne yau, a birnin Beijing. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha daga CMG Hausa)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp